Rundunar ƴansanda a jihar Rivers ta ce ta kama wani dan majalisar wakilai da kudi dalar Amurka dubu 498,100, kimanin naira miliyan 381.1.
Kakakin rundunar yansandan, SP Grace Iringe Koko ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a wani samame da suka kai ranar Juma’a a Fatakwal.
Kakakin ya ce ana binciken dan majalisar ne da laifin karkatar da kudade da kuma yunkurin sayan masu kada kuri’a gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
“Jami’an yansanda da aka tura hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke titin Aba a Fatakwal sun kama shi da karfe 2:45 na safiyar ranar Juma’a.
“Jami’an ‘yan sandan da ke kan bincike sun gano wasu kudade da suka kai dalar Amurka dubu 498,100 a cikin wata jaka a cikin motarsa domin amfani da su wajen zabe.
"Haka kuma an gano cewa akwai jerin sunayen mutanen da aka yi niyyar raba kudin," in ji ta.