Tsohon kwamishinan ma'aikatar addinai na jihar Kano, Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya fice daga jam'iyyar APC, ya koma jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin dan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. A cewar sa waccan tafiyar akwai yaudara a cikin ta sabida haka ba zai yiwu ya cigaba da zama a cikin ta ba.
Ya kuma ce shi dama tun shekarar 2002 shi ɗan asalin ɗariƙar kwankwasiyya ne.