Rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, dan majalisar Doguwa da Tudun Wada daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, yau Talata a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.
Jam'iyyar NNPP ta zargi Doguwa da tada tarzoma biyo bayan ganin rashin nasara a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, ta kuma zarge shi da ƙona magoya bayanta a ofishinta da ke Tudunwada, tare da harbi da Bindiga.
Kawo yanzu dai ba'a bayyana dalilin kamun ba.
Sauran bayanai nanan tafe...