Da Dumi Dumi: Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan manufar musanya naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu
Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan manufar musanya naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka hada.
Kotun kolin da ta saurari karar a ranar Larabar da ta gabata ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello, bi da bi.
A zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN daga yin kwangilar tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.