Kotun ƙoli daka xaman ta a Abuja ta bayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin halastaccen ɗantakara a jam'iyya mai mulki ta APC a Yobe ta kudu.
Kotun koli ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC a Yobe.
Kotun kolin ta amince da daukaka karar da jam’iyyar APC ta shigar kan takarar Bashir Machina.
A hukuncin, uku daga cikin alkalai biyar sun amince da matsayar APC cewa bai kamata a fara karar a kotun ta hanyar sammaci na asali ba tunda ta kunshi zarge-zargen maguɗi.
A cewar kotun kolin, ginshikin karar ya nuna cewa ana tuhumar wadanda suka shigar da kara da maguɗi.