Wata babbar kotun tarayya a jihar Kano, ta bada umarnin a kamo shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tare da bincikensa bisa zarginsa da barazana ga rayuwar mutane, zaman lafiya da kuma furta kalaman tunzura al'umma.
Wani mazaunin jihar Kano mai suna Mahmud Lamido, ne ya shigar da kara ta hannun lauyansa, Bashir Tudun Wuzurci, yana bukatar a kama Abdullahi Abbas bisa barazana da yayi masa ta kisa, ta hanyar kiran waya yana ikirarin "Sai na batar da kai"
Mai shari'a S.A Amobeda na kotun tarayya, ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 16 ga watan da muke ciki na Fabrairu.
Mai magana da yawun jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yace a karo na biyu kenan kotun na bawa kwamishinan yan sandan jihar Kano umarnin a kamo Abdullahi Abbas.