An yiwa kwamishinan yan sandan Kano, CP Mamman Dauda, canjin wanjen aiki zuwa jihar Filato, bayan ƙorafin da jam'iyyar NNPP tayi cewa ya hada kai da gwamnatin jihar Kano ta jam'iyyar APC domin haifar da matsala a zaɓen Kano na 2023.
Sauran bayanai nanan tafe...
Kwankin baya dai anji kwamishinan yana batun cewa kada aga wani ɗan karita ko ɗan bijilanti a filin zaɓe inda wasu suka nuna rashin yardar su.
Haka an gano kwamishinan yana karɓar sabbin motoci ƙirar hilux da fentin ƴansanda daga hannun Barau Jibril Maliya a matsayin tallafi ga ƴansanda.
Sannan jam'iyyar ta NNPP tayi zargin ya kama manya-manyan mambobin ta.
An ɗauke Kwamishinan Ƴansanda na Kano bayan NNPP ta yi ƙorafin ya kama mambobinta
Kwana É—aya bayan da jam’iyyar adawa ta NNPP ta yi kira da a É—auke kwamishinan Æ´ansanda na jihar Kano, Mamman Dauda, bisa zargin nuna son kai, Sifeto-Janar na Ƙasa, Alkali Baba, ya maida shi jihar Plateau domin gudanar da zabe.
A jiya Lahadi ne jam’iyyar NNPP ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin nuna adawa da kamawa da tsare wasu manyan mambobinta sama da 100 da kwamishinan ya yi.
Jam’iyyar ta ce muddin ba a cire CP É—in ba, aka kuma hukunta shi kan rashin da’a da ya yi, za a ci gaba da zanga-zangar.
Sai dai kuma a wata sigina da DAILY NIGERIAN ta samu, Sifeto-Janar din ya mika Dauda zuwa Plateau, sannan ya tura CP Mohammed Yakubu zuwa Kano.
Jaridar Raihana ta ruwaito cewa, IGP din ya kuma tura manyan jami’an ‘yansanda zuwa kowane gundumomi 109 na ‘yan majalisar dattawan kasar nan a lokacin zabe.
A wani sabon sako da aka fitar bayan soke na baya ba zato ba tsammani, IGP ya tura CP Ita Uku-Udom zuwa gundumar Kano ta tsakiya; CP Sunday Babaji mai zuwa mazabar Kano ta kudu da DCP Abaniwonda Olufemi zuwa Kano ta Arewa.