An tashi da baƙin cikin gobara a babbar kasuwar birnin Maiduguri ta Litinin wato (Monday market) wacce ta fara ci tun tsakiyar dare har izuwa yanzu tana ci kuma ba'a shawo ko daƙile ta ba. An tafka babbar asara duba da yadda wutar ke ci ba ji ba gani kuma tana lashe manyan kadarori. Sai dai babu kuɗi cikin abubuwan data cinye izuwa yanzu kasancewar babu abunda ake kira Cash a gari.