Za a sake zaɓe a wasu wurare a Edo
A ci gaba da jawabi da yake yi wa manema labarai na yadda zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya ke tafiya, shugaban hukumar zaɓe farfesa Mahmud Yakubu, ya ce sun samu labaran tayar da rikici a wasu mazaɓu a jihohin Borno da Legas da kuma Bayelsa.
Sai dai, ya ce lamarin ya daidaita.
Mahmud Yakubu ya ce bayan samun matsala ta rashin saka alamar wata jam'iyya a takardar kaɗa kuri'a a wasu mazaɓu biyu na jihar Edo, ya sanya an ɗage zaben sai a ranar 11 ga watan Maris lokacin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jiha.
Ya ce za a yi haka ne saboda kowa doka ta ba shi damar yin zaɓe, don haka INEC za ta yi duk iyawarta na ganin tabbatuwar hakan.
Sannan ya ce a gobe ne za a buɗe karɓan sakamakon zaɓen shugaban ƙasan Najeriya na 2023.
(BBC)