Kamar yadda kowa ya sani hukumar Ƙarbar Ƙorafe-Ƙorafe da daƙile cin hanci da rashawa ta kano, hukuma ce dake ƙoƙarin ganin ta kawo gyara da sauƙi ga al'ummar jihar kano, musamman yayin da ake fama da wani yanayi na matsi a jihar.
A cikin ƙoƙarin mu, mun zagaya gurare daban-daban na kasuwanni ciki har da bankuna da gidajen mai inda muka tabbatar da cewa babu kuɗaɗen da ake zargin bankuna sun ɓoye kuma batun karɓar tsohon kuɗi abu ne da babban bankin ƙasa kaɗai keda hurumin karɓa a gefe guda kuma ƴan kasuwa dake cazar kuɗi sama da kuɗin da aka sayi kayan masarufi ta injinan cire kuɗin su mun kama su kuma yanzu haka muna kan binciiar su kamar yadda doka ta tanada.
A ƙarshe muna masu kira ga al'umma dasu sassautawa kansu su kuma dena amfani da wannan dama ta kuntatawa ƴan'uwan su.