Gwamnatin Kano ta ce zata rufe duk gurin da ya ƙi karɓar tsohon kuɗi a hannun jama'a.
Shugaban Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA Hon. Baffa Babba Dan'agundi ya bayyana haka a yau
Ya ce tuni Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin rufe duk wani gurin kasuwance a faɗin jihar nan wanda yaƙi karbar tsofaffin kuɗi
Baffa Babba ya ce an ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-korafen jama'a da ya yi yawa na ƙin karɓar tsofaffin kuɗin a hannun jama'a musamman a wasu daga cikin gidajen mai da Asibitoci da wajen saye da sayarwa na faɗin jihar nan
Hakan ya biyo bayan umarnin da babban bankin ƙasa CBN ya bayar na ci gaba da karbar tsofaffin kuɗin.
Tuni dai Mai Girma Gwamna ya bayar da umurni ga Kwamitin Kar-ta-kwana mai kula da gidaje Mai su fita su tabbatar ana karɓar tsofaffin kuɗin
Ya bayyana cewa duk wanda yaƙi bin umarnin ya saɓa da dokar Hukumar kula da Haƙƙin mai saye da sayarwa ta Consumer Protection Council, sashe na 10 ƙaramin sashi na 1(b) da kuma sashe na 10 ƙaramin sashi na 2 na dokar Hukumar
Ya ƙara da cewa duk wanda aka kama za a rufe wajen kasuwancinsa tare da gurfanar da shi a gaban Shari'a domin daukar mataki na gaba
Signed
Nabilusi Abubakar
K/Nai'sa
Public Relations Officer
KAROTA
13/2/2023.