Jaridar RAIHANA ta ruwaito cewa ana nuna bacin rai kan sayar da wasu sashe na Makarantu, Asibitoci, Masallatai, da dai sauran su da ake zargin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje mai barin gado ta yi.
A wata sanarwa da kakakin zababben gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar, ya ce duk mutumin da ya saba wa “shawarar”, to kuwa ya yi kasada.
“Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a bayar da wannan shawarar ga jama’a ga duk daidaikun mutane, kungiyoyi da sauran su da suke ci gaba da gine-gine a filayen gwamnati.
“An shawarce ku da ku dakatar da duk wani aikin gine-gine a filayen gwamnati a ciki da wajen Makarantun Jihar, duk wuraren addini da al’adu na Jihar, duk asibitocin Jihar, duk makabartu a Jihar, da kuma gefen badala ta Kano;
“An kuma shawarce ku da ku daina rushewa, da kuma gina duk wasu gine-ginen gwamnati da jama’ar Jihar Kano;
“An bayar da wannan shawarwari ne domin amfanin jama’a, daga yau Alhamis 30 ga Maris, 2023 har zuwa sanarwa ta gaba. Duk wanda ya ƙi ɗaukar shawarar, to yana yin hakan ne bisa ga hadarin kan sa,” sanarwar ta kara da cewa.