Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta shawarci ministar mai jiran gado ta ma’aikatar da kada ta bari a riƙa korar ɗalibai da su ka yi ciki daga makaranta.
Ta ce ilimi shine ginshikin rayuwar ƴaƴa mata.
Tallen ta ba da wannan shawarar ne a wajen wani taron tattaunawa da ma'aikatar harkokin mata ta tarayya ta shirya ranar Juma'a a birnin New York.
Ta ce babu wata yarinya da za a bari a baya in dai Nijeriya na son cimma burin buƙata ta 5 a muradun ci gaba mai dorewa, kan daidaiton jinsi da kuma karfafa dukkan mata da ‘yan mata nan da shekarar 2030.
“Karfafa tattalin arziki ilimi; ba kawai ilimin yarinyar ba, har ma da damar ilimi na biyu ga yara mata da suka yi ciki yayin da suke makaranta.
“sai a kore su daga makaranta a bar mai laifi (wanda yai cikin). Ba ta yi ciki ita kaɗai ba amma wanda ya yi mata ciki za a bar shi a makaranta ita kuma a kore ta.
“Babu wata yarinya da za a kora daga makaranta saboda tana da ciki. Idan an kore ta daga makaranta, shi ma a sallame yaron da yai mata cikin daga makaranta.
"Ya kamata a bar ta ta dawo bayan ta haifi jaririn kuma ta ci gaba da karatunta," in ji ministar.