Wata babbar kotun tarayya da ke Bauchi ta yanke wa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Saleh Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari, bisa samun su da laifin hada baki da kuma karkatar da kudade har Naira miliyan 142,460,000.00.
Mai shari’a Hassan Dikko ya yanke wa mutanen biyu hukunci ne a ranar 2 ga Maris, yayin da yake yanke hukunci kan tuhume-tuhume biyun da Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar wa wadanda ake kara.
An fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar 4 ga watan Yunin 2018 sannan kuma a ranar 16 ga watan Oktoban 2018 aka sake gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu da ake zargin sun karbi sama da Naira miliyan 142 domin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2015 a jihar Bauchi.
Wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, inda suka kafa hanyar da za a ci gaba da shari’ar. A yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaida guda daya da takardun bayar da shaida a matsayin A1, A2 da A3. Dukkan wadanda ake tuhumar sun bayar da shaida a kan tsaron nasu.
A karshen shaidar, an gabatar da bayanai na karshe a rubuce, aka yi musayarsu aka kuma amince da su a ranar 17 ga watan Janairu, 2023, inda masu gabatar da kara suka bukaci kotu da ta hukunta wadanda ake kara kamar yadda ake tuhuma. A daya bangaren kuma, masu tsaron sun gabatar da cewa, shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar a kan wanda ake tuhuma ba su dace ba don haka ya bukaci kotun da ta sallami wadanda ake kara tare da wanke su.
Daga nan Mai shari’a Dikko ya ajiye hukunci a ranar 2 ga Maris, 2023.
Don haka ya yanke wa wadanda ake tuhuma na 1 da na 2 hukuncin daurin shekara 2 a gidan yari ko kuma tarar N3,000,000.00.