Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a yankin Igyorov na karamar hukumar Gboko a jihar Benue, ya dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, lyorchia Ayu, ba tare da bata lokaci ba.
Sun dakatar da Ayu ne saboda nuna adawa da jam’iyyar bayan sun kada kuri’ar rashin amincewa da shi.
A lokacin da yake karanta wani kudiri, sakataren jam’iyyar a gundumar Igyorov, Banger Dooyum, ya ce ayyukan kyamar jam’iyyar Ayu – tare da abokansa – sun taimaka wajen rasa jam’iyyar PDP a mazabarsa da karamar hukumarsa a zaben gwamna. Ana kuma zargin Ayu da rashin biya. hakkokinsa na shekara kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada. Sha biyu daga cikin mambobin exco goma sha bakwai ne suka rattaba hannu kan takardun da ke tabbatar da dakatar da shi.
Sun kuma yi zargin cewa jigon PDP bai kada kuri’a ba a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
A cewarsu, galibin makusantan Ayu sun yi aiki ne da jam’iyyar adawa ta APC wanda hakan ya haifar da dambarwar PDP a yankin Igyorov Ward.
Shugaban gundumar Igyorov, Kashi Philip, shi ma ya sanya hannu kan wasikar tare da exco.
Dubi wasiƙar ta ward exo a ƙasa: