Wata kotu da ke zamanta a yankin Gwagwalada a Abuja, ta tsare wasu makiyaya biyu da suka amsaaifin yin garkuwa da wata mata tare da yi mata fyade a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Maris.
Mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu, wadanda ake zargi, sun yi garkuwa da wata mata mai cikin wata takwas a gidanta da ke Karamar Hukumar Abaji.
Ya bayyana wa alkali cewa wadanda ake zargin sun kuma yi wa matar fyade a cikin dajin, ba tare da la’akari da cewa tana dauke da tsohon ciki ba.
Ya ce wani Abubakar Wakili a Karamar Hukumar Abaji ne, ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan yankin Gwagwalada a ranar 26 ga Fabrairu.