A yau Litinin ne aka gurfanar da wani matashi dan shekara 29 mai suna Olabode Oluosa a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja, bisa zargin satar mota kirar bas din da ta kai kimanin Naira miliyan hudu.
Wanda ake karar, wanda ke zaune a lamba 42 a layin Irepodun Aboru, Iyana Ipaja, Legas ana tuhumar sa ne da laifin sata.
Dan sanda mai gabatar da kara, Raphael Donny ya shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Fabrairu a Oshodi, Legas.
Donny, mai muƙamin sifeto, ya ce wanda ake tuhuma da ke tuka motar bas mallakar mai kara, Lawal Kazeem don yin harkar sufuri, yakan ajiye bas din kowace rana bayan aiki a gidan mai karar.
Mai gabatar da kara ya ce a ranar da aka sace bas din; wanda ake karar ya ajiye motar kamar yadda ya saba amma sai bai ajiye mukulli ba.
Donny ya ce an sace bas din ne jim kadan bayan wanda ake kara ya ajiye bas din kuma ya ki bada ajiyar mukullin.
Ya ce motar bas din ta kai Naira miliyan hudu.
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya sabawa sashe na 287 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, A. O Odubayo ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa.
Mai shari’a Odubayo ya dage sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Maris .