Ƴan Nijeriya ƙalilan ne su ka yarda su dawo gida da ga Tunisia, in ji NiDCOM
Hukumar Kula da Yan Najeriya Mazauna Kasashen waje, NiDCOM, ta ce ‘yan Nijeriya ƙalilan ne suka amince su dawo gida daga Tunisia, biyo bayan kalaman da shugaban kasar ya yi a ranar 21 ga watan Fabrairu.
Shugaban kasar Tunusiya, Kais Saied, a taron kwamitin tsaron kasar, ya yi kira da a dauki matakan gaggawa kan 'yan ciranin da ke kudu da hamadar Sahara.
NAN ya kuma tattaro cewa Saied ya bukaci jami’an tsaron Tunusiya da su dakatar da shige da fice ba bisa ka’ida ba, ya kuma bayyana kwararar bakin hauren a matsayin wata makarkashiyar sauya tsarin dimokuradiyyar kasar.
Shugabar hukumar ta NiDCOM, Abike Dabiri Erewa, a shafinta na Twitter, @abikedabiri, a yau Litinin ta ce Ambasads Asari Allotey, Jakadan Najeriya a Tunisiya, ya na tattaunawa da al’ummar Nijeriya.
“A nan akwai cikakken bayani kan halin da ake ciki a Tunisia, inda bakar fata ke fuskantar hare-haren launin fata. Jakadan namu yana tuntubar al'ummar Najeriya, kan shawarar da aka yanke kan korar mutanen.
“Wadanda suka amince su koma Najeriya kadan ne kuma tawagar tana aiki tare da IOM domin shirya musu tikiti," in ji ta.