Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin kasashen da su ka fi fama da cutar tarin fuka a duniya, in ji Hukumar Kula da Shairin Cututtukan tarin fuka, Kuturta da Olsa, NTBLCP.
Dokta Chukwuma Anyaike, Ko’odinetan Hukumar NTBLCP na kasa ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a kan ayyukan da aka jera domin ranar tarin fuka ta duniya ta 2023 mai taken: “Eh! Za mu iya kawo karshen tarin fuka."
Anyaike ya ce akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan jama’a game da kawo karshen cututtukan da za a iya magance su kamar su tarin fuka da kuma magance mace-mace a kan cutar da sauran cututtukan .
Ya ce, tarin fuka, ya kasance wani babban nauyi a kasar nan wanda za a iya yin rigakafinsa, gano shi, da magani da kuma warkar da shi.
Mista Anyaike ya yi kira ga masu aikin yada labarai da su tsawaita kalmar ‘TB’ zuwa ‘tarin fuka, tare da lura da cewa mafi yawan ‘yan Najeriya ba su da masaniya kan babban nauyin cutar da alamominta.
Shima da ya ke jawabi, Dokta Bethrand Odume Babban Darakta na KNCV Nigeria, ya ce: “Malamai su na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma game da cutar tarin fuka da rigakafinta.
“Mun shirya shirya tarurrukan horaswa ga malamai a makarantu domin kara iliminsu kan cutar tarin fuka da kuma taimaka musu wajen ilmantar da dalibansu,” inji shi
Ya ce hukumar kula da lafiya ta duniya, WHO ta ce mutane 156,000 ne su ka rasu daga tarin duka a 2020, inda ta kama mutane 452,000 a shekarar.