’Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) su 17 da aka ajiye a unguwanni 19 a karamar Hukumar Ideato ta Kudu a Jihar Imo.
An yi garkuwa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa aiki.
Sai dai an tattaro cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ceto su daga baya.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar INEC na jihar, Dr. Chineye Chijioke- Osuji ya ce "an ceto su ba tare da kayan zabe da BVAS ba."