Jihar Bauchi ta samu mutane 7,806 da su ka kamu da cutar tarin fuka a 2022, Dakta Sani Mohammad, babban sakataren hukumar yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, kuturta da zazzabin cizon sauro ne ya bayyana a a jiya Litinin a Bauchi.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na bikin ranar cutar tarin fuka ta duniya ta 2023.
Mohammed ya wakilci kwamishinan lafiya, Dakta Sabiu Gwalabe, a taron na manema labarai.
Ya ce adadin ya karu da 2,154 fiye da 5,652 da aka samu a 2021.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ce ta kebe ranar 24 ga Maris domin bikin ranar tarin fuka ta duniya kowace shekara, da nufin wayar da kan jama'a game da cutar tarin fuka da kuma kokarin kawo karshen ta a duniya.
Ya kuma ce adadin na 2022, wanda ya zama kusan kashi 53 cikin 100 na karuwar matakin cutar a kan na 2021 shi ne mafi girma da aka samu a jihar.
“A cikin mutane5,518 da su je jiyya a 2022, kusan 5,192; wato kashi 94 cikin 100 an yi nasarar yi musu magani a karshen shekara.
“A halin yanzu jihar Bauchi tana da cibiyoyin kula da cutar tarin fuka kyauta guda 794, cibiyoyin bincike 127 da kuma GeneXperts 15,” in ji shi.