Ƙungiyar rajin kawo ci gaba ta YIAGA, ta ce bayanan da ta tattara sun nuna yadda ƴan siyasa suka rinƙa amfani da abubuwa daban-daban wajen sayen ƙuri’a a zaɓen gwamnonin Najeriya.
Jami’in ƙungiyar, Paul James, ya ce sun samu rahotannin sayen ƙuri’u a jihohi da dama, ciki har da irin su Bauchi da Benue.
Ya ce a Makurdi, babban birnin jihar Benue, an rinƙa saya wa mutane barasa domin su kaɗa ma wasu 'yan takara ƙuri’a.
Haka nan a cewarsa an yi amfani da kuɗi sosai a lokacin zaɓen na gwamnoni wanda ya gudana a ranar Asabar.
A tattaunawar da ya yi da BBC a safiyar yau Lahadi, James ya ce babban abin takaicin shi ne yadda wakilan jam’iyyu suka rinƙa kaɗa wa mutane ƙuri’a bayan sun biya su kuɗi.
Ya kuma ƙara da cewa sun samu rahotannin wasu wuraren da aka ƙona ƙuri’u bayan kai farmaki a rumfunan zaɓe.