PRNigeria ta tattaro cewa an gano wasu manyan ma’aikatan hukumar su shida da su ka gyara shekarun haihuwar su, inda aka gano su a yayin jarrabawar ƙarin matsayi a wajen aiki.
An tattaro cewa, Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC, na fuskantar matsin lamba kan ya sassauta wa ma’aikatan da ake tuhuma da laifin.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa PRNigeria cewa ma’aikatan na EFCC da ake zargi da gyarsn kwanan watan haihuwa, sun yi hakan ne don samun wata dama sama da abokan aikin su da su ka yi jarrabawar.
Laifin ma’aikatan shida ya shafi yin ƙaryar shekaru da kuma baiwa kansu damar da ba ta dace ba.
“Kuma sun yi hakan ne ta hanyar canza ranakun haihuwarsu a cikin bayanansu,” in ji majiyar.
Binciken da PRNigeria ta yi ya nuna cewa a baya, an hukunta wasu manyan ma’aikata na EFCC da aka gano sun sauya shekarun haihuwarsu ta hanyar rage musu girma ko kuma tursasa su yin ritaya daga aikin.