Jam'iyya mai mulki ta APC da babbar jam'iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano na musayar yawu wajen zargin juna da amfani da ƴan daba da kuma yin maguɗi a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jiha na ranar 11 ga watan Maris.
Tun da fari, NNPP a wani taron manema labarai da Baffa Bichi, wanda yai takarar Sanatan Kano-ta-Arewa ya jagoranta a yau Litinin, ta zargi APC da dauko hayar ƴan daba zuwa Kano domin su razana masu zaɓe tare da tada hankalin al'umma a ranar zaɓen.
A cewar Bichi, tuni APC ta shirya da wasu wadanda ya kira da gurbatattun jami'an tsaro da na INEC don su yi aringizon ƙuri'u a akwatunan zaɓe.
Ya kuma kara da cewa tuni APC ta shirya da ma'aikatan zaɓe na wucin-gadi, inda har ta basu kafin alkalami da kuma yi musu alkawarin filaye don su taya su yin maguɗin zaɓe.
Hakazalika Bichi ya yi zargin tuni jam'iyyar ta shirya da wani sakatare a INEC, mai suna Garba Lawan, wanda da shi a ka yi maguɗin zaɓen inconclusive domin ya taimaka musu a kuma yin maguɗi a wannan karon ma.
"To wallahi ba za mu yarda ba a wannan karon. Idan ba a dauki mataki ba, to fa yanayin ba zai haifar da ɗa mai ido ba," in ji Bichi.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, kuma Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Gawuna/Garo, Muhammad Garba, shima ya zargi NNPP da dauko hayar ƴan daban domin amfani da su a wajen zaɓe.
Ya zargi NNPP da shirya maguɗi, satar akwatin zaɓe da kone-kone a ranar zaɓe, inda ya ce jam'iyyar su ba za ta bari hakan ya faru ba.
Ya ce duk zarge-zargen da NNPP ta yi ungulu da kan zabo ne domin tuni sun shirya yin maguɗi da tada rikici a lokacin zaɓe.
"Duk wanda aka kama sai an hukunta shi. Ba za mu bari a lalalata harkar dimokuraɗiyya ba," in ji Garba.
Haka itama rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta samu labarin shirin da wasu ɓatagarin ƴan siyasa ke yi n ashigonda ƴan daban a ranar zaɓe.
Sai dai kuma, rundunar ta yi gargadi cewa duk wanda aka kama da yin hakan to fa zai fuskanci hukunci.
Su ma wasu ƴan takarar gwamna a jam'iyyu 9 a yau sun yi zargin yin amfani da ƴan daban daga wasu ƴan siyasa a zaɓen mai zuwa a Kano.