NNPP adawa ta NNPP a jihar Kano, ta rubuta koke ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, inda ta yi tsokaci kan shirin magudin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a jihar.
Takardar koken, mai ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Maris, kuma ta mika wa kwamishinan zabe na jihar, REC, NNPP ta yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa a karamar hukumar Tarauni da ke jihar sun kammala shirye-shiryen hada baki da jami’an zaɓe na INEC, SPOs, domin yin magudi a zabe mai zuwa.
A cikin takardar koken, wacce aka aike wa DAILY NIGERIAN, NNPP ta yi ikirarin cewa bayanan da ta samu sun nuna cewa ana ci gaba da tsare-tsare tsakanin SPO din da wasu 'yan siyasa.
A cewar takardar koken, wani SPO mai lambar waya: 08035179386 ya wallafa sakon WhatsApp, yana tunatar da sauran membobin cewa wani Habu P.A. shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben ‘yan majalisar jiha a kananan hukumomin, inda ya bukaci sauran SPO su tabbatar sun gaggauta tuntubar shugaban karamar hukumar kafin ranar Asabar.
A cikin sakon, SPO din ya ce ba za su karbi ƙasa da dala 5,000 ba a wannan karon.
Jam’iyyar ta yi nuni da cewa, “wasu marasa gaskiya daga cikin SPO sun kuduri aniyar hada kai da APC don dakile sahihancin zabe mai zuwa.”
Don haka NNPP ta yi kira ga REC din da ya dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.