An dakatar da wani dan kwamitin koli na jam’iyyar APC a jihar Kogi, Murtala Yakubu, har zuwa wani lokaci daga jiya Alhamis.
Shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Ajaka Ward 1 da ke karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar Kogi, ya ce an dakatar da Yakubu bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa da wasu laifuka.
Wasikar dakatarwar, mai dauke da kwanan wata 20 ga Maris, 2023, zuwa ga Yakubun mai taken: “Dakatar da ku daga Ajaka Ward 1,” ta samu sa hannun mambobin kungiyar guda 27 daga mazaɓar, ciki har da tsofaffin shugabannin jam'iyyar.
A cikin wasikar, wacce aka kaiwa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Mataimakin Shugaban Arewa ta Tsakiya, Shugaban Kogi, Shugaban shiyyar Kogi ta Gabas da Shugaban Jam’iyyar na Karamar Hukumar Igalamela/Odolu na Jihar kwafi da su amince da dakatarwar Yakubu.
Shugaban mazaɓar ta Ajaka ta 1, Omale Danladi da Sakatare, Suleiman Abubakar, wadanda su ka sanya hannu kan wasikar, sun bayyana cewa an cimma matsayar dakatar da Yakubu ne a yayin wani taro na daukacin shugabannin addu'a, wanda aka gudanar a ranar 17 ga watan Maris a Ajaka.
Sun kuma zargi Yakubu da rashin biyayya, da rashin da’a, rashin gaskiya, tafiyar da tsarin jam’iyya guda daya da kuma karfafa bangaranci a jam’iyyar da dai sauran zarge-zarge.
Sun kuma ce dakatarwar ta fara aiki nan take.