Jam’iyyar APC, reshen jihar Adamawa, ta yi watsi da matakin dakatar da Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, da mazaɓar sa ta Godabawa ta yi a jiya Laraba.
Dr Raymond Chidama, sakataren jam’iyyar APC na jihar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Yola a yau Alhamis.
“ Sanin kowa ne kuma abin da ya kamata a ambata cewa gudummawar da Boss Mustapha ke bayarwa wajen dorewa da kuma tallafa wa jam’iyyar nan ba zai musaltu ba.
“Don haka duk wata kungiya da ta fake wa karkashin jam’iyyar da ‘yan adawa ke daukar nauyin fitowa da munanan zarge-zarge a wannan mawuyacin lokaci, abin alla-wadai ne matuƙa.
"A nan muna bayyana irin wannan dakatarwar ta sabawa kundin tsarin mulki, ba ta kuma da amfani kuma ba ta da wani tasiri," in ji shi.
A jiya Larabane dai shugabannin jam’iyyar APC a shiyyar Godabawa a karamar hukumar Yola-Arewa ta jihar, suka dakatar da Mustapha daga jam’iyyar bisa zarginsa da aikata laifin yinwa jam'iyya zagon-ƙasa.