Wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 a yau Alhamis ya sake fadawa wata babbar kotun Kano cewa bai taba niyyar kashe budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani yar shekara 22, da aka fi sani da Ummita ba.
Wanda ake tuhumar wanda ke zaune a Railway Quarters Kano ana tuhumarsa da laifin kisan kai.
Da kauyan gwamnati, Musa Lawal ke tambayar dalilin da na zuwa gidan su Ummita ba tare da gayyata ba, kuma har ta aiko mishi da fefen bidiyon ta?, sai ɗan China ya kada baki ya ce shi bai yi niyyar kashe ta ba.
“Ban yi niyyar kashe Ummukulsum ba, kuma ba na son a kashe ni. Ta raunata ni a al'aurara kuma ba zan iya nunawa kotu cewa ya saba wa al'adun kasar Sin ba kuma ni musulmi ne.
“A wannan rana mai muni, sai ta kira na ta WhatsApp ta ce in kawo mata karen ta mai suna Charlie.
"Da isa ta gidan su, bayan ta ki daga waya ta, sai na aika mata da sakon tes, daga baya mahaifiyarta (Fatima Zubairu (Pw1)) ta bude gate, na shiga domin na dauko Charlie.
"Ban yi magana da mahaifiyar marigayiyar ba saboda ba ta jin Turanci kuma ni ba na jin yaren Hausa," in ji Frank.
Haka dai aka riƙa titsiye ɗan China a kotun bayan kotun ta karɓi shaidun da aka kawo a kan kisan.
Daga nan sai mai Shari'aSanusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da shari'ar sai ranakun 29 da 30 ga watan Maris.