Wadanda aka ɗauka na daga cikin dalibai 60 da gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunsu a shekarar 2016 domin yin karatun likitanci a kasar China.
Da ya ke zantawa da manema labarai kan ci gaban da aka samu a Dutse a jiya Alhamis, Dakta Salisu Muazu, babban sakatare na ma’aikatar lafiya, ya ce Badaru ya ba da wannan umarni ne bayan mutane 32 da suka ci gajiyar shirin sun ci jarrabawarsu daga Majalisar Likitanci da Kula da Hakora ta Najeriya.
Muazu ya kara da cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin da su ka ziyarci gwamnan a ofishinsa a ranar Alhamis, sun bayyana jin dadinsu da damar da gwamnati mai ci a jihar ta ba su.
Ya bayyana cewa an tura likitocin 32 zuwa asibitin koyarwa na jami’ar tarayya dake Dutse da kuma cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Birninkudu, domin gudanar da aikinsu na horo.
Ya ce idan aka kammala aikin na horo, za a tura likitocin zuwa cibiyoyin lafiya daban-daban a fadin jihar.
A cewarsa, sauran mutane 28 da suka ci gajiyar shirin suma za su shiga aikin horon da zarar sun ci jarrabawar majalisar likitoci da Kula da lafiyar hakora.