Dan takarar majalisar wakilai ta ƙasa na jam'iyyar NNPP a ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Air Commander Salisu Abdullahi Yusha'u Soja mai ritaya, ya ce hankalinsa ya tashi kwarai da gaske bisa abubuwan da ake zargin abokin takararsa na jam'iyyar APC, Alasan Ado Doguwa, ya yi a yankin Tudun Wada, na bada umarnin ƙona ofishin jam'iyyar NNPP, dukda yasan cewa akwai mutane a ciki.
Soja ya bayyana haka ne cikin zantawa da manema labarai, inda yace duk wani mutum mai imani bai ji dadin abinda aka yi musu, kuma kamata yayi Alasan din ya tunkare shi ba yaje ya afkawa wadanda basu ji ba basu gani ba.
Yace tuni aka miƙa shi gaban kotu, kuma suna da yaƙinin za a dauki mataki a kansa.
A karshe Soja yayi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma jajantawa ga wadanda suka jikkata.