Ko kun san cewa idan Gawuna yaci gwamna a Kano ya rusa mafarkin Barau Jibrin Maliya na son zama gwamna a shekarar 2027.
Barau ya nemi takarar gwamna a shekarar 2023 wanda saboda son gwamnan yasa sai da yayi faɗa da Ganduje aka raba gari aka samu rabuwar kai tsakanin ƴan jam'iyyar ta APC a lokacin. Wasu suka bi ɓangaren gwamna inda suke iƙirarin cewa Abdullahi Abass ne shugaban jam'iyya ɓangaren su Barau kuma suke iƙirarin cewa mamman ɗanzago shine shugaban jam'iyyar ta APC a kano. Inda a ƙarshe kotu ta tabbatar da Abdullahi Abass na ɓangaren Gwamna. Har yanzu Barau yana da burin zama gwamnan kano a shekarar 2027 idan kuma Gawuna yaci a kano wannan shekarar babu wannan burin na Barau saboda zai nemi komawa kan kujerar sa dole. Saboda haka ana zargin Barau ba zai marawa Gawuna baya don ya samu gwamna wannan karon ba saboda ya samu damar kasancewa JAGORA na jam'iyyar a Kano sai abunda yace har izuwa lokacin da za'a kaɗa gangar siyasa ta shekarar 2027.