Ma’aikatan wucin-gadin da su ka zanta da manema labarai sun ce ba a biya su alawus-alawus na horo da na zabe na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da suka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
Cikin nuna takaici, ma’aikatan sun yi ƙorafin cewa duk da tsananin damuwa da barazana ga rayuwarsu, har yanzu ba a biya su cikakken alawus-alawus din su ba.
Jaridar RAIHANA ta ruwaito cewa, akwai fargabar cewa karancin naira da ake fama da shi a kasar nan zai shafi biyan ma’aikatan da ke yi wa hukumar aiki.