Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta ce za ta haɗa wa Musulmai buɗe-baki a filin wasa na Stamford Bridge a watan Ramadan.
Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa ita ce ta farko a Gasar Firimiya da za ta haɗa buɗe-bakin na kowa da kowa tare da haɗin gwiwar gidauniyar Ramadan Tent Project.