A cikin kirarin, wanda aka aika wa Jaridar Raihana a jiya Laraba, Abdullahi ya zargi tsohon shugaban TETfund, Baffa Bichi, da jagorantar harin.
A cikin karar mai dauke da sa hannun lauyoyinsa Salisu Muhammad Lawal da Ibrahim Abere, shugaban ya ce harin ya faru ne a lokacin da Bichi ya jagoranci yakin neman zaben jam’iyyar zuwa mazaɓar Kutama da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar. Ya yi zargin cewa Bichi ya jagoranci wasu jami’an NNPP irin su Nasir Sule Garo, Kabiru Haruna, Abdullahi Kwami da Umaru Danmakau zuwa garin al’umma, inda suka yi amfani da muggan makamai, ciki har da bindigogi.
Koken ya ce a lokacin da suka kai harin, nan take suka harbe mutum daya mai suna Abdullahi Shuaibu, wanda ya mutu a asibiti a Gwarzo.
Takardar ta kuma yi zargin cewa magoya bayan NNPP sun harbi wasu jama’a da suka hada da Malam Umar, Ibrahim Umar da Babangida Ado, inda suka samu raunuka daban-daban a kafafunsu.
Shugaban ya kuma yi zargin cewa magoya bayan jam’iyyar NNPP sun kai wa gidansa hari ta hanyar kona wani sashi daga gidan.
Acewarsa, wadanda lamarin ya rutsa da su yanzu haka suna asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda suke karbar kulawa bayan an kai su asibitin Gwarzo.
Don haka masu shigar da karar sun bukaci ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin domin kaucewa tabarbarewar doka da oda.
Tsohon sakataren zartarwa na TETfund din bai amsa waya da sakon kar-ta-kwana da wakilinmu ya aika masa ba domin neman jin ta bakinsa a bisa zarge-zargen.