Charles Aniagwu, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, PCC, na jam'iyyar PDP, ya ce matakin dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu haramtacce ne.
Mista Aniagwu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Asaba, inda ya ce wadanda suka yi wannan dakatarwar sun jahilci tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Ya ce sashe na 57(7) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ya fito karara kan wanda ke da ikon dakatarwa ko ladabtar da wani dan kwamitin koli na kasa ko kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa.
“Lokacin da su ka je su ka nemi mazabar shugaban jam'iyyar na kasa da ta dauki matakin ladabtarwa a kansa, ganin cewa suna da ikon ya kamata su yi masa adalci ta hanyar kiransa da su ba shi damar kare kansa.
” Amma sashe na 57 bai basu ikon aiwatar da irin wannan mataki a kan dan kwamitin koli, NWC ba.
"Saboda haka, idan wani ya kai kara kotu da irin wannan dakatarwar ba bisa ka'ida ba, kawai yana so ya haifar da matsaloli ne ga jam'iyyar," in ji shi.