Farfesa Mohammed Mele, jami’in zaben INEC na jihar ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a jiya Litinin a Yola.
Mista Mele ya ce an soke zaben a wuraren rijistar zabe 47, da rumfunan zabe 69 da ke da adadin masu kada kuri’a dubu 41,796.
“adadin katin zabe na dindindin (PVCs) daga rumfunan zabe da abin ya shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa sun kai dubu 37,016.
“Bayan tattara kuri’u mun kididdige adadin kuri’un da ‘yan takara biyu da ke kan gaba a zaben suka samu, inda APC ta samu dubu 390,275, PDP ta samu kuri’u dubu 421,524.
“Don haka wannan ya bada tazarar dubu 31,249 kuma adadin PVC da aka tattara a wuraren ya kai dubu 37,916,” in ji shi.