Gwamna Nyesom Wike na Rivers ya ce bai goyi bayan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi karara ba a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu domin babu wanda ya tattauna da shi kan takarar Igbo.
Sakataren yada labarai na kungiyar Ohaneze Ndigbo na duniya, Dr Alex Ogbonnia ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a Enugu cewa Wike ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar ta yi da shi a Fatakwal a jiya Alhamis.
Ogbonnia ya bayyana cewa, a wajen taron, Ohaneze Ndigbo ta fuskanci Wike a kan zargin da ya yi wa Obi a lokacin zaben shugaban kasa.
Ya bayyana cewa Wike ya bayyana mamakinsa cewa Ohanaeze na kokarin gano gaskiya kuma zai bayyana irin rawar da ya taka a zaben shugaban kasa.
A cewar Ogbonnia, gwamnan Rivers ya bayyana cewa kungiyar gwamnonin kudu sun fara ganawa ne a Asaba inda su ka amince cewa mulki ya koma Kudu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya kuma bayyana cewa daga baya gwamnonin sun hadu a Enugu a watan Satumba na 2021 don tabbatar da matsayinsu na komawa Kudu.
Ya bayyana cewa a duk tarukan da aka yi, “ba a taɓa tattauna batun shugabancin yankin Kudu-maso-Gabas ba," inji shi