Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta dakatar da zaben ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a jihar Sokoto a ranar 25 ga watan Fabrairu, sabo da ta gano wasu kura-kurai a cikin zaben.
Manjo Janar Modibbo Alkali mai ritaya, kwamishinan hukumar ta INEC na kasa da aka sake tura wa domin sa ido a jihar ne ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a yau Laraba a Sokoto.
Alkali ya ce gano hakan ya sa aka tsige kwamishinan zabe na jihar, REC, da dai sauransu.
Ya yi alkawarin cewa hukumar za ta karfafa tsarinta domin gyara kura-kuran da aka samu tare da tabbatar da cewa zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da za a yi a ranar 11 ga watan Maris zai kasance mai inganci.
“INEC ta lura da abubuwan da ba su dace ba a kan lokaci kuma ta yanke shawarar dakatar da zaben ƴan majalisar tarayya na ranar 25 ga Fabrairu a jihar Sokoto."