Dalilin da ya sa na janye buƙatar duba kayayyakin zaɓe - Atiku
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya janye karar da ya shigar gaban kotun daukaka kara kan bukatar duba kayan zabe ne saboda wasu abubuwa da suka dabaibaye kudirin.
A wata sanarwa da ya fitar, Abubakar ya ce tuni hukumar zabe ta kasa INEC ta ba shi damar duba kayan, inda ya kara da cewa hakan ne ya sanya ya janye kudirin nasa.
Ya ce wannan bayanin na da muhimmanci biyo bayan batanci da rahotanni na karfe da su ka biyo bayan janye bukatar ta sa ta neman hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta baiwa tawagar lauyoyin sa da jam’iyyar PDP damar duba takardun da su ka shafi zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu. .
A tuna cewa kotun daukaka kara ta amince da bukatar jam’iyyar PDP da Abubakar na a ba su damar duba takardun INEC ba tare da wata matsala ba.