Abdullahi Abacha, wanda shi ne ɗa na biyun-ƙarshe ga marigayi tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya , Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36 a duniya.
Iyalin Abacha sun tabbatar wa Jaridar Raihana rasuwar a yau Asabar, inda suka ce Abdullahi ya rasu ne cikin barci a a gidansu da ke titin Nelson Mandela a Abuja.
“A daren jiya fa lafiyar sa kalaunya kwanta, amma yau da safe sai gawarsa a ka samu. Ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barcinsa,” in ji wata majiya daga iyalin Abacha.
Jaridar Raihana ta tattaro cewa za'ayi Jana'izar sa da misalin karfe 4 na yamma a babban masallacin kasa dake Abuja a yau Asabar.
An haife shi a shekarar 1987, marigayin yana daya daga cikin yara tara da marigayi shugaban soji ya bari.