Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a Lokoja.
A ranar Laraba ne dai kotun kolin ta yanke hukuncin ci gaba da amfani tsofaffin takardun kudin Naira na N1000, N500 da N200 tare da takardun kudi da aka sabunta har zuwa Disamba 2023.
Gwamnan ya bayyana ce ba za a manta ba kuma “rashin biyayya ne”, kin karɓar tsohon kudin duk da hukuncin da kotun koli ta yanke.
“Wannan gwamnatin ba za ta tsaya kallon yadda wasu mutane da ‘yan kasuwa ke ci gaba da kin karɓar tsohuwar takardar Naira ba, duk da hukuncin kotu da ta tabbatar da amfani da su.
A gare mu, kin amincewa da tsofaffin takardun Naira, rashin biyayya ne ga hukuncin da Kotun Koli ta yanke, wanda ya kamata a daƙile.
“Duk wanda ya ki karɓar tsohuwar takardar naira, a kai rahoto ga jami’an tsaro da na gwamnati domin a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.