Mataimakin gwamna kuma dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam'iyyar APC a zaɓen shekarar 2023 da za'a gudanar Ranar Asabar 18 ga watan Maris, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ja kunnen jami'an tsaro cewa su tsaya akan gaskiya.
Gawuna ya bayyana haka ne ranar Asabar a ofishin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC dake Kano, inda yace ya kamata abar kowa yayi zaɓensa, kada a hana kowa.
"Wallahi babu wanda ya isa a jami'an tsaro yazo yanzu, ya ce ga abu na rashin gaskiya wai zai goyi bayansa, da iznin Allah zamu yi masa sanadin ya rasa kakinsa, ya tsaya yayi gaskiya, bamu ce mu yayi mana rashin gaskiya ba."
"Babu wani wanda muka ce yazo mu ya kare ya hana mu, ko kuma ya hana wasu suyi zaɓen su, kowa a barshi yayi zaɓensa."