Gwamnatin Tarayya ta ce an ƙiyasta cewa aikin ƙidayar jama'a da za a gudanar a ƙasar zai laƙume naira biliyan 869.
Hakan ne nufin an ƙiyasta cewa za a kashe dala shida kan kowanne mutum guda, kwatankwacin kusan naira 2800.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa, Prince Clem Ikanade Agba ya ce ya gana da masu ruwa da tsaki wajen tattauna shirye-shiryen ƙidayar jama'ar da za a gudanar cikin wannan shekara.
Ya ce kuɗin da za a kashe a kan kowanne ɗan ƙasar, ya yi sauƙi idan aka kwatanta da abin da ake kashewa a ƙasashen Amurka da Botswana, waɗanda ke kashe dala 16, da dala 10 a kan kowanne mutum a ƙidayar.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya ta bayar da kashi 46 na kuɗin da ake buƙata domin gudanar da aikin ƙidayar, inda yanzu hukumar ke jiran gudunmowa daga jihohi da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tabbatar da nasarar aikin.