Gwamnatin tarayya ta amince da kashe biliyan 24.2 domin saka intanet kyauta a filayen jirgin sama 20, jami'o'i da kasuwanni
Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da wasu kwangiloli biyu na Naira biliyan 24.20 don samar da manyan hanyoyin sadarwa na intanet kyauta a wuraren taruwar jama’a 75 da suka hada da filayen jiragen sama 20 da manyan makarantu da kasuwanni a fadin kasar nan.
Ministan Sadarwa da Bunkasar Tattalin Arziki daga Fasahar Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala taron na FEC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa jiya Laraba a Abuja.
Dukkanin ministocin da suka yi magana a taron manema labarai bayan FEC sun ce an amince da jimillar Naira biliyan 209.36 don gudanar da ayyuka daban-daban a ma’aikatun su.
Da ya ke bayyana amincewar ma’aikatarsa, Pantami ya ce takardun yarjejeniya guda biyu na da alaÆ™a, tunda dukkansu sun mayar da hankali ne kan samar da ayyukan haÉ—a yanar gizo kyauta.
Ministan ya ce takardar yarjejeniya ta biyu ta kasance mai kamanceceniya da amincewa hakan a bara.