Hajjin 2023: Hukumar alhazai ta Kano ta bukaci maniyyata da su cika kuɗinsu ya kai Naira miliyan 2.5
Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta yi kira ga maniyyata, musamman waɗanda su ka ajiye Naira miliyan 1.5 a matsayin adashin gata da su gaggauta cika wa ya kai Naira miliyan 2.5.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Ilmantarwa da Wayar da Kai, kuma Kakakin hukumar, Hajiya Hadiza Abbas Sanusi a yau Alhamis.
Ta yi kira ga maniyyatan da su cika kuɗin ya kai adadin miliyan biyu da rabi kafin daga bisani Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta ayyana tsayayyen farashin aikin Hajjin 2023.
Ta kara jaddada cewa maniyyatan su cika kuɗin kafin nan da zuwa 5 ga watan Afrilu.
Haka zalika Hadiza ta kuma yi kira ga maniyyatan da ba su kai fasfunan su hukumar ba da su gaggauta kai wa domin a yi aiki a kan su.