Abba Yusuf Bichi, dan babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS, Yusuf Bichi, ya yi watsi da cecekucen da ake yi a kan sa cewa ya na goyon bayan jam'iyyar APC da dan takararta a zaben shugaban kasa da aka kammala.
Jaridar Raihana ta tattaro cewa an fara cecekucen ne ta yanar gizo jim kadan bayan hukumar SSS ta fitar da wata sanarwa inda take zargin wasu bata-gari ’yan siyasa na kulla makarkashiyar hana rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da kuma kafa gwamnatin riƙo a kasar.
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi watsi da sanarwar ta SSS tare da yaɗa hotunan matashin Bichi na yakin neman zaben APC.
Don haka sun ke zargi hukumar da cewa ta saki sanarwar me saboda tana goyon bayan jam'iyya mai ci.
Amma da ya ke mayar da martani ga masu suka ta hanyar shafinsa @Abba_Yusufbichi, Bichi, wanda ya shahara da bayyana salon rayuwarsa ta kasaita a shafukan sada zumunta, ya yi tambaya kan cewa ko ya rasa ƴancin sa na kasancewarsa dan DG SSS.
“Barka da safiya ’yan Najeriya, saboda mahaifina shi ne DG na DSS, to kai tsaye ƴanci na ya ƙare a matsayina na dan kasar nan kenan? Ma'ana ba zan iya goyon bayan kowace jam'iyya ba saboda mahaifina? Shin ba ni da ƴanci a matsayina na ɗan ƙasa in zaɓe wanda nake so?” in ji shi.