Kotu ta aike da wani matashi gidan yari bisa zargin satar akwatin zaɓe a Kano
Kotun Majistre mai lamba 14, karkashin jagorancin alkali Mustapha Sa'ad Datti, ta aike da wani matashi zuwa kurkuku bisa zargin sa da kwace akwatin zaɓe, takardun dangwala kuri'a da kuma inkin dangwala kuri'a .
Lauya mai gabatar da kara, Barista Hajara Ado Saleh a jiya Juma'a ta shaidawa kotun cewa, matashin Ibrahim Jibrin Birged, ya shiga cikin makarantar firamare ta Gama, ƙaramar hukumar Nassarawa, tare da kwace akwatin zaɓen da sauran kayan zaɓe.
Sai dai kuma ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.
Alƙalin ya ɗage sauraron shari'ar zuwa 8 ga watan Maris, ya kuma bada umarnin a ci gaba da tsare matashin a gidan yari.