Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bai wa ɗan takarar shugaban Najeriya a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Labour, Peter Obi damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu.
Tun farko ƴan takarar ne daban-daban suka miƙa buƙatar neman a ba su damar duba kayayyakin da aka yi amfani da su a babban zaɓen 2023 tare da tilasta wa INEC ta ba su damar ganin kayan aikin da aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasar.
A ranar Laraba 1 ga watan Maris ne Atiku Abubakar ya shigar da tasa ƙarar yayin da Peter Obi kuma ya shigar da tasa ranar Alhamis biyu ga watan.
Kan haka ne kotun ta umarci hukumar zaɓe ta bai wa ɗan takarar PDP damar duba kayayyakin zaɓen.
A yau Juma'a kuma kotun ta amsa bukatun 'yan takarar na duba kayan zaɓen sannan kuma su titsiye hukumar zaɓe kan wasu bayanai da za su buƙata.
Kotun ƙarƙashin mai shari'a Joseph Ikyegh ta bayar da umarnin ne bayan da ta saurari wasu ƙararraki da ƴan takarar biyu suka shigar tare da jam'iyyunsu.
PDP da LP waɗanda a baya-bayan nan suka yi watsi da sakamakon zaɓen, sun ce samun damar ganin kayayyakin za ta taimaka musu a ƙalubalantar sakamakon zaɓen da suke yi wanda ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.
A cewar INEC, Tinubu ya ci zaɓen ne da ƙuri'u 8,794,726 inda Atiku Abubakar na PDP yake bi masa da ƙuri'u 6,984,520 sai Obi na Labour Party da ya zo na uku da ƙuri'u 6,101,533.