An gurfanar da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa a gaban wata kotu a jihar Kano bisa laifuka masu alaƙa da haɗin baki wajen aikata kisan kai.
Saurn laifukan da ake zarginsa da sun sun haɗa da raunata mutane da da dama, tare da zargin hannu a kunna wuta a ofishin jam'iyyar hamayya ta NNPP.
Tayar da gobarar a ofishin a ranar Lahadi 26 ga watan Fabarairu, 2023 ya yi sanadin ƙona wasu mutane da ke cikin ofishin.
A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar da ke lura da al'amuran zaɓen 2023 CP Muhammad Yakubu ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge zargen.
Laifukan sun haɗa da kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a ranar, a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.
An yi ta yaɗa hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta, inda daga nan kuma rundunar 'yan sandan ta gayyaci ɗan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.
Sanarwar ta ce bayan da ɗan majalisar ya ƙi amsa gayyatar ne, rundunar 'yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.