Ƴansanda ne su ka gurfanar da Bello mai shekaru 30 da Umar mai shekaru 26 bisa samun su da laifin hada baki, tsoratarwa, zamba, sata da kuma karbar kudi ta karfi.
Alkalin kotun Majistare, Munir Sani ne ya yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin bayan sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, tare da rokon a yi musu sassauci.
Sani ya yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso kan kowane laifi ba tare da zabin biyan tara ba.
Ya kuma umurci wadanda aka yankewa hukuncin da su biya diyyar Naira dubu 165,000 ga wadanda suka kai kara.
Tun da fari, Lauyan masu shigar da kara, Abdullahi Tanko ne ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 3 ga watan Fabrairu a ofishin ‘yan sanda na Gwagwalada, ta hannun Mista Muhamodu Bello da Usman Dikko, na kauyen Dukpa Gwagwalada, Abuja.
Tanko ya ce a ranar 21 ga watan Janairu wadanda aka yanke wa hukuncin da kuma wani Umar, wanda ya tsere, sun hada baki, sun shiga gonar wani Bello (mai kara na farko) inda suka sace shanu 14 da kudinsu ya kai Naira miliyan 2.5.
Ya ce daga baya wadanda aka yanke wa hukuncin sun kira shi suka bukaci a ba su N250,000 kafin su sako masa shanun.